Dakarun rundunar Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutane 22 da aka sace tare da dakile wasu yunkurin garkuwa da mutane a kananan hukumomin Sabon Birni da Isa na jihar Sokoto.
Mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanar Aliyu Danja, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 18 ga Yuni bayan jamiāan tsaro sun samu bayanan sirri da kiraye-kirayen neman agaji daga alāummomin da abin ya shafa.
A cewarsa, āyan taāadda sun tare hanyar Sabon Birni zuwa Shinkafi a kauyen Kura Mota, inda suka kai hari kan motoci biyu tare da yin garkuwa da fasinjoji. Ya ce mutum daya ya rasa ransa kafin sojoji su isa wurin.
Danja ya bayyana cewa sojojin sun kaddamar da farmaki tare da taimakon jiragen sa ido, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa tare da barin mutane 17 da suka sace.
Haka kuma, sojojin sun ceto wasu manoma biyar a kauyen Chohi da ke karamar hukumar Isa bayan āyan bindiga sun yi yunkurin yin garkuwa da su a gonakinsu.
Rundunar ta ce ta kara gudanar da sintiri a wasu kauyuka domin kwantar da hankalin mazauna yankunan da kuma hana sake kai hare-hare, tana mai jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin alāumma a yankin Arewa maso Yamma.
Daily Nigerian


