26.6 C
Kano
Wednesday, March 11, 2026

Sanata Natasha ta shiga office a yammacin Talata kuma tace ba zata baiwa majalisa haƙuri ba

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta isa ginin Majalisar Taraiya a yau Talata, inda ta shiga ofishinta bayan kammala hukuncin dakatarwar watanni shida da aka yi mata.

Yayin da ta ke magana da yan jarida, Mrs. Akpoti-Uduaghan ta ce ba za ta nemi afuwa daga Majalisar Dattawa ba, kasancewar ta tsira daga abin da ta kira rashin adalci da aka yi mata.

A cewarta,  rashin adalci tsantsa hana ta komawa bakin aikinta na majalisa saboda akwai shari’a da ke gudana a kotu kan lamarin.

“Har yanzu ina jiran wasiƙar (na dawowa aiki) domin yana da matuƙar muhimmanci a fahimci sharuddan da za su iya sanya – ko da kuwa ba bisa doka ba.

“Saboda na karanta a jaridu cewa an yi taron shugabanni a jiya, kuma shugaban marasa rinjaye, Sanata Abba Moro, zai gabatar da ƙuduri a ranar 7 ga Oktoba yana kira gare ni da in nemi afuwa.

“Don haka ina matuƙar damuwa game da irin afuwar da suke tsammanin zan nema. Ba za ka nemi afuwa ba kan irin wannan rashin adalci da aka yi maka,” in ji ta.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa