Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta gargadi majalisar dokoki cewa za ta fito da mambobinta yin zanga-zanga idan aka ci gaba da hana Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, komawa bakin aiki bayan dakatarwar da aka kammala.
Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya fitar da sanarwar ne a ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa ci gaba da tsare mata hanya ya saba wa tsarin dimokuradiyya, yana mai cewa abin da ya faru da dan majalisa guda na iya zama hari kan ’yan Najeriya baki daya.
Sai dai har yanzu ba a bayyana ko NLC za ta fito da gaggawa yin zanga-zanga idan aka cigaba da hana sanatar dawowa aiki ba, musamman ganin an rage jiran hukuncin kotu kan dakatarwar.
A farkon makon nan kuwa, lauyar Sanata Natasha ya yi barazanar kai kara gaban kotu idan aka hana ta komawa bakin aiki kafin Litinin mai zuwa.


