Shugaban rukunin kamfanonin kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya alƙawarta sake rage farashin shinkafa da sauran kayan abinci, wanda ya ce tun shekarar da ta gabata yake ta sauka.
Abdul Samad Rabiu ya bayyana haka ne ranar Alhamis jim kaɗan bayan ganawarsa ta Tinubu a fadar shugaban ƙasar.
Shugaban na BUA ya yaba wa Tinubu kan bayara da damar shigo da wasu kayan abinci da ya yi, yana mai bayyana matakin da ‘kyakkyawa” da ya ce ya taimaka wajen karyewar farashin kayan abinci a ƙasar.
A watan Yulin 2024 ne gwamnatin Shugaba Tinubu ta bayayna dakatar da karɓar kudin fito na shigo da kayan abinci a wani mataki na magance hauwarar farashin kayayyaki.
BUA ya zargi masu sayen kayyaki domin ɓoyewa da haddasa tashin farashin.
Ya ce da zarar lokacin girbe amfanin gona ya yi, sai wasu su riƙa sayen kayan suna ɓoyewa, har tsawo wata uku, daga baya kuma su fito da kayan su tsawwala farashi domin sayarwa kamfanonin sarrafa abinci .
To sai dai ya ce bayan matakin shugaban ƙasar, kamfanonin sarrrafa shinkafa sun shigo da wadataccen kaya, lamarin da ya sa dole masu ɓoye kayan suka fito da nasu suna sayarwa a farashi mai sauƙi.
”Wannan shi ne abin muka yi, kuma za mu ci gaba da yin haka domin mara wa matakin gwamnati baya na tabbatar da farashin abinci ya sauka, kuma na tabbata farashin zai ci gaba da sauka”.
Kalaman BUA na zuwa ne a daidai lokacin da rahoton hukumar Ƙididdiga na ƙasa NBS ke nuna cewa an samu raguwar farashin kayyaki a ƙasar a watan Afilu idan aka kwatanta da watan Maris da ya gabata.