Idan za’a iya tunawa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar da mataimakiyarsa da yan majalisar dokokin jihar bayan sanya dokar ta-ɓaci a jihar Rivers bayan rikita-rikitar siyasa da jihar ta daɗe tana fama da shi.
Shugaban ya ayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a kan matsalar siyasar da ke addabar jihar ta Rivers.
Gwamnan jihar Siminalayi Fubara da majalisar dokokin jihar sun kasa samun fahimtar juna a tsawon lokaci.
Bayan nazari kan halin da ake ciki a jihar Rivers, ya zama wajibi na sashi na 305 na ayyana dokar ta-ɓaci daga yau 18 ga watan Maris, 2025
An dakatar da gwamnan Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa na tsawon wata shida.
Tinubu yace yayi iyakar bakin kokarinsa kan yadda za a magance matsalar to amma duka bangarorin sun yi watsi da yunkurin nasa
Haka nan shugaban ƙasa ya bayyana cewa wasu mutane daga ɓangarori daban-daban su ma sun yi nasu kokarin amma babu mafita.
A yanzu ta tabbata babu wata sahihiyar gwamnati a jihar Rivers.