Fadar Shugaban kasa ta ce yawancin kuɗaɗen da aka fitar daga Babban bankin Najeria (CBN) ƙarƙashin shugabancin Godwin Emefiele, an fitar da su ne ba tare da sa hannun tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba.
Ajuri Ngelale, mashawarci na musamman ga shugaba Bola Ahmad Tinubu, kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kan jama’a ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi a shirin With Chude na Chude Jideonwo wanda aka watsa a gidan talabijin na Channels.
BBC Hausa ta rawaito cewa Ngelale ya ce dole ne gwamnatin da ta gabata ta ɗauki alhakin wasu abubuwan da suka faru a babban bankin ƙarƙashin jagorancin Emefiele.
Ngelale ya jaddada cewa, yayin da Buhari ya samu nasarori a wasu fannonin samar da ababen more rayuwa, rashin sanya ido kan al’amuran Babban bankin ya taimaka wajen taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasar.
Duk da cewa ya amince cewar Bola Tinubu ya bai wa gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari goyon baya, Ngelale ya ce a yanzu Tinubu na ƙoƙarin ganin ya magance matsalolin da suka haifar da taɓarɓarewar tattalin arzikin kasar da ta faru a zamanin gwamnatin Buhari.
Ngelale ya yi nuni da cewa Buhari ne ya yanke shawara dangane da tsawaita wa’adin mulkin Emefiele, duk kuwa da cewa shugaban bai san al’amuran da ke gudana a Babban Bankin.