Shugaban Najeriya, Bola Tinubu na ziyarar aiki a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin ƙasar.
Tinubu na ziyarar ne domin ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar, Sanat Uba Sani ya aiwata tsawon shekara biyu da ya shafe yana mulkin jihar.
Cikin ayyukan da shugaban ya ƙaddamar sun haɗa da wani asibitin ƙwararru mai gadaje 300 da gwamnatin jihar ta gina don bunƙasa harkokin lafiya.
Haka kuma shugaban ya ƙaddamar da cibiyar koyar da sana’o’i, sai kuma motocin safa masu amfani da iskar gas ta CNG guda 100.
Shugaba Tinubu na samun rakiyar mataikaminsa na musamman kan harkokin siyasa, Sanata Ibrahim Masara, da mai taimaka masa kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu da wasu jiga-jigan gwamnati.
Haka kuma shugaban ya samu tarba daga gwamnan jihar Kaduna tare da takwarorinsa na makwabtan jihohi.
Ziyarar shugaban na zuwa ne kwana guda bayan ziyarar jaje da ya kai jihar Benue da ke fama da rikice-rikice