34.8 C
Kano
Sunday, September 7, 2025

Ma’aikatan Jinya da Ungozoma Sun Janye Yajin Aiki – Ministan Lafiya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Ma’aikatan Jinya da Ungozoma sun dakatar da yajin aikin da suka fara a fadin ƙasar nan, bayan cimma matsaya da shugabannin ƙungiyar su.

Ministan Lafiya, Farfesa Ali Pate, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma’a, jim kaɗan bayan wata ganawa ta bayan ƙofa da jagororin Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Ƙasa (NANNM).

A cewarsa, dakatar da yajin aikin ya biyo bayan sahalewar da aka cimma tsakanin wakilan gwamnati da shugabannin ƙungiyar, wanda ya kawo ƙarshen shan wahala a cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati a faɗin ƙasa.

Sai dai, shugabannin ƙungiyar sun ƙi yin tsokaci ga manema labarai bayan kammala taron.

Ma’aikatan jinya da ungozoma sun fara yajin aikin gargadi ne a ranar 29 ga Yuli, 2025, bisa zargin gazawar gwamnatin tarayya wajen mayar da martani kan wa’adin kwanaki 15 da ƙungiyar ta bayar tun a ranar 14 ga Yuli.

Yajin aikin wanda aka tsara ya dore har zuwa 5 ga watan Agusta, ya janyo cikas a ayyukan kula da lafiya a asibitocin gwamnati, inda marasa lafiya da dama suka fuskanci jinkiri a jinya.

Ƙungiyar ta bayyana cewa yajin aikin ya samo asali ne daga matsalolin da suka dade suna addabar ma’aikatan jinya da ungozoma, musamman rashin kyawun yanayin aiki, ƙarancin alawus, da sakacin gwamnati wajen inganta walwalarsu.

Daga cikin muhimman buƙatunsu akwai, ƙarin alawus na aiki da dare, daidaita kuɗin tufafi, tsarin albashi na musamman, ƙarin alawus na aiki na musamman, ɗaukar sabbin ma’aikata, da ƙirƙirar sashen kula da su a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Morakinyo Rilwan, ya sha alwashin cewa gwamnati ba ta ɗauki matakin tattaunawa da ƙungiyar ba har sai da yajin aikin ya fara.

“A halin da ake ciki, babu wani kiran tattaunawa daga gwamnati. Shi ya sa muka ci gaba da yajin aiki. Sun samu isasshen lokaci amma suka yi shiru,” in ji Rilwan a wata sanarwa da ya fitar a baya.

Ya kuma bayyana cewa matakin shiga yajin aikin ya samo asali ne daga matsin lamba daga mambobin ƙungiyar a fadin ƙasa, sakamakon dogon lokaci suna fuskantar ƙalubale da rashin kulawa daga gwamnat

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa