- Hon Nasir Bala Aminu Jaoji yace yanzu ne ma lokacin da ya kara saka ‘danba don taimakon ‘ya’yan jamiyyar APC tare da saka su cikin walwala.
Nasiru Jaoji ya bayyana hakan ne a yau yayin da yake kaddamar da rabon motoci ga jagororin jamiyyar APCn yankin karamar hukumarsa ta Tarauni.
Jaoji yace zaa taimaki ‘ya’yan jamiyyar don tabbatar da cewa dan jamiyyar APC bai yi kuka ba don haka an bada motocin kyauta don aikin jamiyyar.
Da yake jawabi yayin kaddamar da rabon motocin shugaban jamiyyar APC na Kano Abdullahi Abbas ya bukaci Hon jaoji da fitowa da kayan abinci don rabawa ‘ya’yan jamiyyar saboda kusantowar azumi
Abdullahi Abbas ya ce Wannan shi ne bambancin jamiyyar APC da jamiyyar Adawa ta NNPP