Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatin sa na kammala dukkan shirye-shirye da suka dace don gabatar da kasafin kuɗi na farko a tarihin jihar mai darajar Naira triliyan 1 na shekarar 2026.
A yayin bude Taron Majalisar Zartaswa ta Musamman ta Biyu, Gwamna Yusuf ya ce girman wannan kasafi yana nuna azancin gwamnati wajen aiwatar da manyan ayyuka, gyaran birane, da fadada ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
Ya bayyana cewa karuwar kasafin kuɗin na 2026 ta samo asali ne daga inganta hanyoyin samun kudaden shiga na cikin gida da kuma dakile duk wata asarar kudade, wanda hakan zai ba gwamnati damar aiwatar da manyan ayyuka masu sauyi a jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa kasafin zai mayar da hankali kan ci gaban gidaje, aikin gona, ilimi, lafiya, da tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu, domin bunkasa tattalin arziki da samar da hanyoyin dogaro da kai ga al’umma.
Za a mika kasafin kuɗin ga Majalisar Dokokin Jihar Kano domin yin nazari da amincewa.
Gwamna Yusuf ya kuma sake tabbatar da niyyar gwamnatin sa ta gudanar da mulki cikin gaskiya, kula da kudade yadda ya kamata, da tallafawa dukkan sassan gwamnati domin samar da ingantattun ayyuka ga jama’a.
Idan aka amince da shi, wannan zai kasance kasafin kuɗi na farko da kowace jiha ta Arewa a Najeriya ta samar.


