20.9 C
Kano
Saturday, January 17, 2026

Farashin kiret ɗin kwai zai iya kai 10,000 – Masu kiwon kaji

Ƙungiyar masu kiwon kaji ta Najeriya ta ce nan ba da jimawa ba kiret ɗin kwai zai iya kai naira 10,000.

Ana dai sayar da kiret ɗaya tsakanin N5,500 zuwa N6,000 a yanzu.

Najeriya na fama da hauhawar farashi mafi muni wanda ba a gani ba cikin shekaru inda farashin kayayyaki ke tashin gwauron zabi a kullu yaumin.

Wasu dai na danganta hakan da tsadar man fetur da kuma ƙarancin kuɗaɗen waje.

Da yake magana a wani taro domin tunawa da ranar kwai ta duniya a Abuja, sakataren ƙungiyar ta PAN a babban birnin tarayya, Musa Hakeem, ya buƙaci gwamnati ta ayyana dokar ta-ɓaci a fannin noman kwai.

BBC ta ruwaito Ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ba ta ɗauki matakin gaggawa ba, farashin kwai zai ci gaba da tashi wanda kuma zai ƙara jefa ƴan Najeriya cikin kunci.

Hakeem ya danganta ƙaruwar farashin da tsadar kuɗin sufuri sakamakon cire tallafin man fetur, da kuma hauhawar farashin kayan abinci.

“Hakan zai iya sa farashin kwai ya koma 10,000, duk da cewa yanzu muna sayar da shi a kan 5,500,” in ji shi.

Ya kuma nuna rashin jin daɗinsa kan rashin samun tallafi daga gwamnati, inda ya ce an kai sehkara uku rabon da masu kiwon kaji su samu wani tallafi.

Hakeem ya buƙaci cewa a ƙara karfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu kiwon kaji, tare da jaddada cewa ƙungiyar na da dabaru waɗanda za a iya amfani da su wajen magance matsalar.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa