Daga Abba Anwar, Kano
Maganar cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kuma Mataimakin Farko Na Kakakin Majalisar Kasashen ECOWAS Sanata Barau Jibrin shine jagoran APC a jihar Kano ko ba shi ba ne, ba ita ce maganar yi ba yanzu. Kawai dai ita maganar ta na bukatar fahimta ingantacciya tare da bayanai sahihai.
Kawai dai kasancewarsa shine kololuwar zababbu masu rike da mukamai a matakin kasa, wani abu ne da yake bukatar tattaunawa wajen abinda ya shafi yanayin mulki da tasirin mukami a madafun iko.
Tun ma kafin wannan lokaci na sha kai korafi ga wasu jagorori yadda wasu da suke kusa da tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje suke kokarin kai shi rami dan su hallaka shi. Ko kuwa yadda wasun su suke taimakawa wajen hallaka shi a siyasance. Wannan ba wani abu ne boyayye a wajen kowa.
Kuma babban abin bakin cikin kuma shine yadda wasu makusantan nasa suke kau da kai tare da banzantar da yadda ya kamata a kawo masa kariya da dauki lokacin da makiyansa da ‘yan adawarsa ke hayyake masa ta kafafen sadarwa.
Mai karatu zai iya tuna lokacin da tsohon shugaban karamar hukumar Nassarawa, Auwal Shuaibu Aranposu ya dirarwa Baba Ganduje. Abin mamaki a lokacin kadan ne daga cikin yan soshiyal midiya din mu su ka tashi haikan dan kare mutuncin Ganduje. Da yawa daga cikinsu, sun fi samun tallafi daga Aranposu din kan yadda masu kula da harkokin yada labaran Baba Ganduje suke mu’amalantar su. Duk fa da kasancewarsa shi Aranposu din dan adawa ne daga jam’iyyar NNPP.
Bari mu ajiye maganar Aranposu haka. Wani babban abin takaici da Allah wadai shine lokacin zabubbukan fitar da ‘yan takara na
zaben kananan hukumomi na birnin tarayya Abuja, an yi kokari an sa wasu daga cikin ‘yan soshiyal midiya, amma saboda bakin cikin za su dan samu wasu ‘yan kudaden aikin zaben a ka fitar da sunayen su daga tsarin.
Saboda tsananin kyashi da muguntar kar su karu da dan alawus alawus da a ke bayarwa. A ka cire sunayen su da kuma sunayen wasu mutanen mu daga jihar Kano. Duk irin wadannan abubuwan su na nuni da cewar irin wadannan makusantan Baba Ganduje ba zaman amana suke da shi ba.
Kuma wani babban abin takaici da tir da Allah wadai shine, wasu da suke manne da shi su na hallaka shi tare da danna shi a ramin siyasa ba ma ‘yan Kano ba ne kwata-kwata. Ko da ya zama shugaban jam’iyya na kasa, tattare da hobbasa din sa da fito da sabbin tsare-tsaren gyaran jam’iyya, amma duk da haka irin wadannan mutane sai su ka kara daura damarar hallaka shi. Har ma ta kai ta kawo a ka kara samo wasu sabbin ‘yan gangan a harkar. Zaman karya da cin amana.
Idan mu ka dawo maganar Barau, da ganin yadda abin yake gudana kowa ya san da cewa, kaddarar rayuwa ce da kariya daga Allah kawai suke tafiyar da bawan Allan nan.
Ba boyayyen abu ba ne, kowa ya san yadda makiya APC da ci gaban jam’iyyar suke ta kutun-kutun hada Barau rigima da wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyya kuma jagorori masu mutunci da girmama dan Adam. Wannan abin fa da nake fada a fili yake kowa ya sani kuma kowa ya gani.
Sai fa da ta kai ta kawo an hada rigima tsakanin Barau da tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomi kuma tsohon dan takarar Mataimakin Gwamna a zaben 2023, kakkarfan bawan Allan nan kuma mai fada a ji da son ci gaban jama’a, wato Murtala Sule Garo.
Amma cikin hukuncin Allah da kuma iya shugabanci na Baba Ganduje da wani zabe ya zo, sai da Gandujen ya sa Garo ya zama babban daraktan kamfen na Barau. Cikin Ikon Allah da iya tsarin tafiyar da al’umma na Garo, sai Allah Ya ba Barau nasarar cin zaben nasa na Sanata.
Gaskiyar zance Barau ya ga duk wani nau’i na wulakanci da nuna bai isa ba. Sakamakon kulle-kullen makirci na wasu daga cikin makusanta Baba Ganduje. Amma Allah Ya sa masa hakuri da juriya da kamewa. Har a ka kawo wannan gwadaben da a ke kai yanzu.
Kuma dan a kara cakuda abubuwan, lokacin da Ganduje zai gama gwamnatin sa a karo na biyu, sai ya yi yadda ‘yan uwansa gwamnoni ke yi idan sun gama zango na biyu a mulki, ya so ya tsaya takarar Sanata daga Kano ta Arewa. Wato mazabar da Barau ya fito. Daga nan kuma sai makiya da magabta a ka bude wani sabon shafi na haddasa zazzafar adawa da kiyayya tsakanin Ganduje da Barau.
Sai da ta kai ta kawo Barau ya je ya yi kulle-kullennsa daga Abuja ya samo tikitin takararsa. Amma kasancewar Ganduje dattijo ne kuma mai son ci gaban jam’iyyar, ya zo ya marawa Barau baya, kamar yadda ya yi a baya. Har a ka samu nasara. Ba wanda ya isa ya dauke wannan yabo daga Ganduje. Duk kin ka da Allah kuwa.
To ina jin daga lokacin ne Baba Ganduje ya fara duba gefensa dan ya fahimci su waye ke tattare da shi. Amma su kuma masu zama da shi ba da zuciya daya ba, su ka yi farat a na ba shi shugabancin jam’iyya na kasa su ka kara samo sabbin ‘yan gangan dan a ci gaba da danna Baba a rami.
Wani abin yabawa kuma da ba ka isa ka dauke daga Ganduje ba shine, yadda ya hada hannu da Barau dan kara firgita ‘ yan adawa a Kano. Sai fa da kai ta kawo, dukkan wani abin rashin jin dadi da ya shafi gwamnatin Kano ta NNPP ko wani jami’in gwamnati sai a ce Ganduje.
Idan misali wani ya rasa raka’a daya a kowace Sallah cikin salloli biyar, sai su ce “Ganduje.” Idan matar wani ma ta yi bari wajen haihuwa sai su ce “Ganduje.”
Hayaniyar masarauta a Kano, su ce “Ganduje.” Zaman Sarkin Kano Aminu Ado Bayero a Gidan Nassarawa, su ce “Ganduje.” Rashin iya mulkinsu ma su ce “Ganduje.” Shi fa Baba Ganduje ya sa musu wani irin tsoro da firgici zartacce mara kaidi.
To amma cikin kaddarar rayuwa da yadda Allah Ya tsarawa Barau a tafiyar sa ta siyasa, wadda ta samo asali shekaru da yawa da su ka wuce, bisa doron hakuri da juriya da bibiyar abubuwa yadda suke, sai haka kawai Allah Ya sa masa wani karfi da hobbasa rabbaniyyi, sai ya kasance irin suka da adawa da gwamnatin Kano da magoya bayan ta ke wa Ganduje, yanzu an tattara su sun fuskanci Barau gaba daya. Haka kaddarar rayuwa take.
Daga cikin ire-iren masu ganin Barau bai isa ba a jam’iyyar APCn, suke ganin kuma waye shi, har sun fara lababawa da rarrafawa wajen sa. Wasun su a boye a boye. Kuma ire-iren wadanda ke zama ba na amana ba da Ganduje har da su a wannan bigiren.
Daga bayanan da nake da alfarmar samu, na fahimci cewar ba tun yau ba, tuntuni Barau ya fara samum fahimtar juna da ire-iren mutanen da a ka dinga hada su fada da shi. Amman fa wadannan mutanen su ne masu tsayawa kaifi daya da kaunar jam’iyyar tare da su. Ba ‘yan gangan marasa zaman amana ba.
Yadda nake kallon abin kuma nake fahimtar abin shine, yadda Barau ya dago sama haka, ba tsimi ba dabara kawai daga Allah ne. Ni haka na kalli abin.
Har yanzu kuma ina mamaki idan mutane na cewa su ba su ga irin su wane su wane a wajen Barau ba. Ya dai kamata su fahimci cewar, kowane dan siyasa fa ya na da irin nasa salon na tafiyar da harkokin siyasar sa.
Ni dai na san Barau ya fi shekara 40 ya na siyasa. To me kuma yake bukata kafin a ce ya iya siyasa ko ya fahimci mecece siyasa?
Wani abu kuma da zan fada shine, na san yadda wasu ke ta yin rawar kafa wajen kwararowa zuwan wajen Barau. Da ‘yan gaske da’ yan gangan gaba daya. Babban abin farincikin shine, shi Barau ya san me yake so. Kuma a wajen wa. Kuma ta yaya yake son wannan abin.
Da jimawa na san Barau ya na kallo tare da nazarin wadanda ke tattare a wajen Ganduje. Ya san kyawunsu da muninsu. Ya san amfanin su da rashin amfanin su. Ba wai ba inke.
Kasancewar jam’iyya APC ba kamar sauran jam’iyyu ba, na san har yanzu ta na da damar kara habaka da cigaba daga dukkan bangarorin rayuwa. Wannan ba wai ba ne, haka maganar take. Illa iyaka.
Shi kuma Barau a nawa ganin da kuma hangen, shi kawai Ikon Allah ne. Kuma wata aya ce da Allah ke son nuna wani abu ga mutane da shi.
Anwar ne ya yi wannan rubutun daga Kano
4 ga Juli, 2025


