Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta rushe shugabancin kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar ADC karkashin Sanata David Mark, tare da soke duk wasu matakai da kwamitin ya dauka a madadin jam’iyyar.
Hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu ya yanke ya shafi zaben fidda gwani da ya tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2027 mai zuwa.
Atiku, wanda a baya hukumar zabe ta INEC ta wallafa sunansa a matsayin dan takara, ya riga ya zabi tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, a matsayin mataimakinsa kafin wannan hukunci na kotu.
Shari’ar ta samo asali ne daga karar da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar Arewa maso Gabas, Nafiu Bala Gombe, ya shigar yana kalubalantar yadda kwamitin Sanata Mark ya karbi ragamar shugabanci bayan murabus din tsohon shugaba Ralph Nwosu.
Sai dai jam’iyyar ta ADC ta bayyana cewa ba ta gamsu da wannan hukunci ba, inda sakataren jin dadin jam’iyyar na kasa, Nkemakolam Ukandu, ya tabbatar da cewa za su daukaka kara zuwa kotun gaba.
Share


