26.5 C
Kano
Saturday, September 6, 2025

Ba a Yi Adalci Ga Musulman Najeriya Ba Kan Juma’a A Matsayin Ranar Aiki – Reno Omokri

Tsohon mai ba wa shugaban ƙasa shawara, Reno Omokri, ya bukaci a yi gyara kan tsarin ranakun aiki a Najeriya domin bai wa Musulmai damar gudanar da sallar Juma’a ba tare da cikas ba.

A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya Juma’a, Omokri ya bayyana cewa tsarin yanzu rashin adalci ne, yana mai cewa kafin mulkin mallaka, Juma’a ta kasance ranar hutu ga Musulmai.

Ya ce bai dace ba a bar Lahadi a matsayin hutu ga Kiristoci yayin da ake tilasta wa Musulmai yin aiki a Juma’a.

“Ina ganin ba a yi wa al’ummar Musulmi adalci ba mu kasance da Juma’a a matsayin ranar aiki a Najeriya. A asali, kafin mulkin mallaka, ba haka abin yake ba,” in ji Omokri.

Omokri ya bayar da shawarar a daidaita lokutan aiki yadda ofisoshi za su rufe da wuri a Juma’a, yayin da Litinin zuwa Alhamis za a fara aiki da wuri domin ba wa ma’aikata damar gudanar da ibada

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa