Kungiyar Nas ta kasa sun jaddada cewa su fa har yanzu basu janye Yajin aiki da suka tsunduma ba.
Kungiyar tace ayi watsi da rahotonnin da Ministan Lafiya Farfesa Muhammad Ali Paté ke yadawa cewa an cimma matsaya, Kungiyar ta dakatar da yajin aiki.
A cewar kungiyar har yanzu basu cimma wata matsaya ba kan yiwuwar janye Yajin aikin dasuka tsundima sakamakon wasu dalilai.