20.9 C
Kano
Saturday, January 17, 2026

Kamala Harris ta yi alkawarin sauya salon mulkin Amurka idan ta lashe zaɓe

Ƴar takarar shugabancin Amurka a jam’iyyar Democrat, Kamala Harris, ta yi alƙawarin sauya salo daga irin kamun ludayin shugaba Joe Biden, idan har ta samu nasara a zaben da za a yi a wata mai zuwa.

A cikin hirarta ta farko da tashar Fox News mai ra’ayin mazan jiya, wacce aka tsara don tattaunawa da yan jam’iyyar Republican da ke da tantama kan abokin hamayyarta Donald Trump, Madam Harris ta ce tana wakiltar rukunin matasa shugabbannin gobe ne.

BBC ta ruwaito ta ce ”kamar kowanne sabon shugaban ƙasa, nima zan shigo da tawa kwarewar da na samu a tsawon rayuwata.”

Ta yi ta zazzafar muhawara da jagoran tattaunawar Bret Baier na tashar Fox, a lokuta da dama musamman kan batun shige da fice

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa