32.9 C
Kano
Friday, January 16, 2026

Bobrisky ya ɗaukaka ƙara don ƙalubalantar hukuncin ɗaurin wata shida

Fitaccen mai amfani da shafukan sada zumunta, Idris Olanrewaju Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky ya ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin kotu da ta same shi da aikata laifuka hudu da ke da nasaba da wulaƙanta takardun naira.

A ƙarar da ya shigar ta hannun lauyansa, Bimbo Kusanu, Bobrisky na neman kotu ta jingine hukuncin wata shida a gidan yari da aka yanke masa tare da neman kotu ta ba shi zaɓin biyan tarar naira dubu 50 kan duka laifukan da aka same da saikatawa.

A ranar 12 ga watan Afrilu nemai shari’a Abimbola Awogboro na tabbatar kotun tarayya a Legas ta yanke wa Bobrsiky hukuncin wata shida a gidan yari ba tare da zaɓi biyan tara ba saboda wulaƙanta naira.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa yayin yanke hukunci, mai shari’a ta ce hukuncin zai zama izina ga sauran mutane da suka saba wulaƙanta naira.

A ranar 5 ga watan Afrilu, Bobrisky ya amsa aikata laifuka huɗu da hukumar EFCC ke tuhumarsa da aikatawa

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa