24.1 C
Kano
Monday, January 12, 2026

Nijar ta sake bude iyaka da Najeria

Jamhuriyar Nijar ta sake buɗe kan iyakarta da Najeriya a yankunan Diffa da Tahoua da Maradi da Dosso.

An rufe iyakar kasar da ke tsakanin makwabtan biyu biyo bayan juyin mulkin da aka yi a ranar 26 ga watan Yuli da kuma takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakaba mata.

BBC A wani sakon rediyo da aka watsa a shafukan sada zumunta, a ranar Alhamis, ma’aikatar harkokin cikin gida ta Jamhuriyar Nijar ta umurci gwamnonin waɗannan yankuna na kan iyaka da su ba da izinin sake bude aiki da karfe 12:00 na dare.

Ma’aikatar ta kuma umurci gwamnonin da abin ya shafa da su karfafa tsaro a kan iyakokin kasar.

An buɗe iyakokin Najeriya makonnin da suka gabata bayan ɗage takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakabawa ƙasar a wani taro da aka yi a Abuja, amma Nijar ba ta mayar da martani ba nan take.

Sai dai kuma har yanzu kan iyakar Nijar da makwabciyarta Benin na nan a rufe a ɓangaren Nijar duk da gaggawar aiwatar da umarnin ECOWAS da hukumomin Benin suka yi.

Hukumomin rikon kwaryar Nijar sun bayar da dalilai na tsaro a matsayin dalilin rashin buɗe kan iyaka da makwabtanta da ke Kudu

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa