35.1 C
Kano
Monday, January 19, 2026

Yanzu Yanzu: Gwamnan Kano Ya Shiga Ganawa da Shugaba Tinubu a Villa

Ganawar ta gudana ne a ofishin shugaban ƙasa, inda Gwamna Abba Yusuf ya isa fadar da misalin ƙarfe 4:10 na yamma, sanye da farar babban riga (Agbada) tare da hular ja, abin da ya ja hankalin masu bibiyar al’amuran siyasa.

Tun makonnin baya, ana ta rade-radin cewa gwamnan Kano na dab da sauya sheƙa zuwa APC, lamarin da ya haifar da cece-kuce da rabuwar kai a tsakanin magoya bayansa, musamman dangane da alakarsa da jagoran siyasar NNPP kuma uban gidansa na siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Rahotanni sun nuna cewa tattaunawar sauya sheƙar ta ci karo da tangarda, sakamakon rashin jituwa kan batun tabbatar wa Gwamna Abba Yusuf tikitin takarar gwamna kai tsaye a zaɓen 2027, wanda ake cewa ya zama babban sharaɗi a cikin tattaunawar.

Masu sharhi na siyasa na ganin cewa wannan ganawa da Shugaba Tinubu ba ta rasa nasaba da shirin sauya sheƙar, duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance daga bangarorin biyu har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa