29.3 C
Kano
Friday, April 4, 2025

Yanzu Babu Sarki A Kano – Shugaban Masu Rinjayen Majalisar Dokoki

A cewar shugaban masu rinjaye na majalisar Lawal Hussaini Chediyar Yan Gurasa, wannan matakin na nufin cewa a halin yanzu babu sarki a jihar Kano.

Dokar Sarakunan Jihar Kano da aka fara samar da ita don samar da masarautu biyar, yanzu an soke

“Wannan kudiri, gaba dayansa, ya soke kafa sabbin masarautu guda biyar, ya koma tsarin gargajiya na sarki daya, tsarin da aka yi shi tun a Jihadin Shehu Usman Dan Fodio,” in ji Lawal Hussaini.

Sabuwar dokar dai ta baiwa gwamnan Kano ikon nada sabon sarki ta hanyar gayyatar masu nada sarki su zaba daga cikin takara. “Da soke karin masarautun, babu sarki a Kano.

Yanzu ya rage ga gwamna ya yanke shawarar lokacin da zai nada sabon Sarkin, kamar yadda sabuwar dokar ta tanada.” Inji Lawal Hussaini.

“Wannan gyara da akayi na da nufin dawo da hadin kai a Kano, wanda a cewar dan majalisar, ya ruguje sakamakon samar da masarautu biyar,” Lawan Hussaini.

Dokar da ta gabata wacce tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sanya wa hannu a ranar 5 ga Disamba, 2019, ta samar da karin masarautu guda hudu, daga nan kuma ta kai ga tsige Alhaji Muhammadu Sanusi, Sarkin Kano na 14.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa