21.9 C
Kano
Sunday, January 18, 2026

Waiya ya lashi takobin inganta Lafiyar al’ummar jihar Kano

Kwamishinan Ma’aikatar yada labarai da harkokin cikin gida ta jihar kano Comarade Ibrahim Abdullahi Waiya ya bukaci Jami’an yada labarai na kananan hukumomin jihar da su cigaba da aiki da Kwarewa wajen wayar da kan al’umma musamman kan batun da ya shafi inganta harkokin kiwon lafiyar al’umma.

” Babu shakka za mu cigaba da baku dukkanin gudunmawar da kuke bukata domin ganin Kuna cigaba da gudanar da aikinku bisa Kwarewa da kuma tallafawa gwamnati da al’ummar jihar Kano baki daya”

Bayanin Kwamishinan ya zo ne yayin bude taron bita ta yini biyu ga Jami’an yada labarai na kananan hukumomi 44, domin inganta Kula da abinci mai gina Jikin dan adam.

Ya kara da cewar, ana sa ran bayan kammala bitar Jami’an yada labaran za su yi amfani da Ilimin da suka samu wajen wayar da kan al’ummar kananan hukumomin da suke aiki saboda su rika cin Abinci mai gina Jiki, don magance matsalar mace-macen da ake samu a Kano saboda wasu cututtuka da suke da alaka da cimak”.

Waiya ya ce ya gamsu da rawar da Jami’an yada labaran suke takawa wajen ganin sun sauke nauyin da aka dora musu, wanda ya ce hakan ce ta sa tunda ya Zama Kwamishina ya ke shirya musu bitoci don kyautata aiyukansu .

“Ina kira a gare ku da ku rika amfani da damarku wajen Isar da sakonni ko wayar da kan al’umma, yayin duk wani taron da ake yi karamar hukumar da ku ke aiki, hakan zai taimakawa wajen Kai sakonninku cikin al’umma cikin sauki” . Inji Waiya

Kwamishinan ya kuma ce daga yanzu zai saka gasa a tsakanin Jami’anta yadda duk wata za a rika fitar da wadanda suka fi yin kwazo a watan , inda ya yi alkawarin ba da kyauta ga wadanda suka yi nasara.

Wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana gidiyarsu ga kwamishin bisa yadda ya shirya musu bitar , inda suka ce sun amfana Sosai da bitar kuma za su duk mai yiwuwa don aiwatar da abun da suka koya .

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa