Tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya kamu da cutar Kansar mafitsara kamar yadda ofishinsa ya fitar da sanarwa.
Tsohon shugaban da iyalansa na nazari kan matakin dauka na maganin cutar tare da kwararrun likitoci.
A sanarwar da ofishin Mr Biden ya fitar ya ce ya je asibiti domin yi masa gwaje-gwaje sakamakon matsalar da ya ke samu wajen yin fitsari, anan ne likitoci suka gano akwai wani kullutu a marainarsa.
Bayan karin gwaji aka tabbatar ya kamu da mummunar nau’in cutar kansar mafitsara da ta fara yaÉ—uwa zuwa kashinsa.