26.5 C
Kano
Saturday, September 6, 2025

Tinubu ya umarci asibitocin tarayya su rage farashin wankin ƙoda

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da rage farashin wankin ƙoda daga naira 50,000 zuwa naira 12,000 a manyan asibitocin tarayya a fadin ƙasar.

Daniel Bwala, mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan Bayanan da suka shafi tsare-tsaren gwamnati ne ya bayyana hakan a shafin sada zumuntansa na X, inda ya ce matakin zai sauƙaƙa wa dubban marasa lafiya masu fama da ciwon ƙoda.

An fara aiwatar da wannan mataki a manyan asibitoci kamar FMC Ebute-Metta da ke Lagos da FMC da ke Jabi a Abuja da UCH Ibadan da FMC Owerri da UMTH Maiduguri, yayin da za a ƙara wasu kafin ƙarshen shekara domin samun damar amfani da su a duk faɗin ƙasar.

Shugaba Tinubu a baya ya amince da haihuwa ta hanyar tiyata kyauta a asibitocin gwamnati domin inganta lafiyar mata da rage mace-macen da za a iya hana faruwarsu.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa