Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da bai wa sojoji 17 da aka yi wa kisan gilla a yankin Neja Delta lambar girmamawa ta kasa da kuma alkawarin gina wa kowanne gida a inda suke so tare da bai wa ‘yayansu tallafin karatu har zuwa matakin jami’a.
Tinubu ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi yayin gudanar da jana’izar sojojin sojoji 17, inda ya bayar da umarnin cewar hukumomin soji su tabbatar da cewar an biya hakkokin wadannan soji nan da watanni uku.
Tinubu ya bayyana cewar shugaban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya masa bayani a kan irin gagarumar gudumawar da Laftanar Kanar Ali, kwamandan sojin da aka kashe ya bayar wajen yaki da Boko Haram da kuma ‘yan bindiga a yankin Arewa Maso Yamma, kafin mayar da shi yankin Neja Delta.
Shugaban ya ce a madadin Najeriya yana mika sakon jinjina ga Kanal Ali saboda yadda ya bayar da gagarumar gudumawa a rundunar sojin har zuwa lokacin da aka yi masa kisan gillar