28 C
Kano
Friday, January 16, 2026

Tinubu ya cire Maryam Sanda daga jerin waɗanda aka yiwa afuwa

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya cire sunan Maryam Sanda daga jerin waɗanda ake shirin yi wa afuwar shugaban ƙasa.

An dai tuna cewa kotu ta yanke wa Maryam hukuncin kisa a shekarar 2020 bayan ta tabbatar da cewa ta kashe mijinta, marigayi Bilyaminu Bello.

A cewar wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mista Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba, Shugaba Tinubu ya bada umarni cewa duk wanda aka samu da manyan laifuka irin su garkuwa da mutane, safarar miyagun ƙwayoyi, safarar mutane, zamba, da kuma mallaka ko safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba, a cire su daga jerin sunayen waɗanda ake son yi wa afuwa.

Sanarwar ta bayyana cewa, maimakon a saki waɗanda aka saka sunansu a tsohon jerin afuwa, gwamnati za ta sake nazarin hukuncinsu ne domin rage masa kaɗan, ba wai a sakesu gaba ɗaya ba.

Fadar shugaban ƙasa ta ce wannan sabon mataki yana da nufin tabbatar da cewa tsarin bayar da afuwa yana gudana cikin gaskiya da adalci, tare da kare mutuncin tsarin shari’a da kuma tabbatar da amincewar jama’a da shi.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa