34.8 C
Kano
Sunday, September 7, 2025

Tinubu ne zai karɓi gawar Buhari a Katsina

Shugaban Nigeria Bola Tinubu ne zai tarbi gawar tsohon shugaba Muhammadu buhari a Katsina, domin yi masa jana’iza a Daura.

Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris ne ya tabbatar da hakan da yammacin yau Litinin a Abuja.

A cewar ministan, da misalin karfi 12 ranar gobe Talata ake saran gawar marigayi tsohon shugaban ya isa Katsina.

Sannan za a yiwa shugaban faretin ban girma a filin jirgin saman Katsina, kafin daga bisani a wuce garin Daura da gawarsa.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima yanzu haka na Landan, kuma shi ne zai rako gawar har Katsina.

Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamiti na musamman da za su tsara jana’izar da kuma duk wani abu da ake bukata wajen binne shugaban.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa