24.1 C
Kano
Monday, January 12, 2026

Tinubu Bashi Da Hannu A Rikice-Rikicen Da Su Ka Dabaibaye Jam’iyyun Adawa – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Kasa ta musanta zargin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da hannu a rikicin da ke addabar wasu daga cikin jam’iyyun adawa a Najeriya, tana mai bayyana zargin a matsayin zance maras tushe.

Mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabarun mulki, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da tashar Arise News a shirin Prime Time a daren ranar Alhamis 10 ga Yuli, 2025.

Onanuga ya karyata rahotannin da ke cewa Shugaba Tinubu yana tsoma baki a cikin harkokin taruka da ayyukan jam’iyyun adawa, musamman hadin gwiwar da ke faruwa tsakanin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar; dan takarar jam’iyyar Labour Party, Peter Obi; da wasu a karkashin tutar African Democratic Congress (ADC).

“A Najeriya yanzu akwai wata dabi’a da mutane ke da ita na alaƙanta kowacce irin matsala da Tinubu. Duk inda aka samu cikas sai a ce shi ne ke da hannu. Amma ba gaskiya ba ne. Wasu daga cikin abubuwan ma sun faru ne a lokacin da baya cikin ƙasa,” in ji Onanuga.

Shugabannin jam’iyyun adawa sun zargi cewa wuraren da suka kama domin gudanar da taruka ana soke su, inda wasu daga cikin ‘yan hadin gwiwar ADC suka ce dole ne su yi tafiya mai nisa zuwa cibiyar Shehu Musa Yaradua a Abuja don guje wa shiga hannun jami’an tsaro da kuma yiwuwar toshe hanyoyin shiga.

Sai dai Onanuga ya musanta zargin cewa gwamnati na kokarin hana adawa ko murkushe ‘yancin fadin albarkacin baki.

“Wannan gwamnati na baiwa mutane damar fadar albarkacin bakinsu. Na ji wasu suna cewa gwamnati na hana ‘yancin magana – wannan karya ce. Gwamnatin nan ta na mutunta ‘yancin fadi, ‘yancin ra’ayi da ‘yancin kafafen yada labarai. Idan wani otal ya soke taro, sai a ce Tinubu ne ya mallaki otal din?” a cewar Onanuga.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa