24.1 C
Kano
Monday, January 12, 2026

Shugaban Ƙasa Ba Shi Da Iko Tsige Gwamna

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce shugaban ƙasa ba shi da hurumin tsige ko da kansila da aka zaɓa, balle gwamna, yana mai cewa wannan abu ya sabawa tsarin mulkin Najeriya.

Shettima ya fadi hakan ne yayin da yake tuna wani yunkuri da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya yi domin tsige shi daga kujerarsa ta gwamnan Jihar Borno a shekarar 2012, lokacin da rikicin Boko Haram ya fi kamari.

A cewarsa, Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya a wancan lokaci, Mohammed Bello Adoke, ne ya hana hakan, yana mai jaddada cewa shugaba ba shi da irin wannan iko a tsarin mulkin ƙasa.

“Shekara ta 2012 lokacin ina gwamna, shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya so cire ni daga kujerata. Amma Adoke, wanda shi ne Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya a wancan lokaci, ya ce masa shugaban ƙasa ba shi da ikon tsige ko da kansila da aka zaɓa, balle gwamna,” in ji Shettima.

Maganar Shettima na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da takaddama a siyasance kan rawar da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya taka wajen dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Rivers daga wasu manyan ayyuka da yake yi, tare da shisshigi a rikicin siyasar jihar.

Masu fashin baki na ganin cewa kalaman Shettima wata gargadi ce ga masu son shugaba ya wuce iyakar ikon da kundin tsarin mulki ya tanada masa. Suna jaddada cewa dole ne a mutunta ikon jihohi da kuma ‘yancin zababbu bisa kundin tsarin mulki.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa