27 C
Kano
Sunday, January 18, 2026

Shekarau ya magantu kan batun sake hadewarsu da Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekaru ya ce yana da kyakkyawar alaƙa tsakaninsa da da jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

A hirarsa da BBC, Malam Shekarau ya nuna babu wata tattaunawa da nufin sulhu tsakaninsa da Rabiu Musa Kwankwaso, saɓanin rahotannin da ke cewa suna tattaunawa.

Ya ce babu wani sulhu tsakaninsa da jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

“Ni ban ma yarda a yi amfani da kalmar sulhu ba tsakanina da ɗan’uwana Rabiu Musa Kwankwaso ba.”

“Duk inda ka ji an ce sulhu, to rigima ake yi,” in ji Malam Shekarau.

Malam Ibrahim Shekaru ya ce babu wata matsalar dangantaka tsakaninsa da Kwankwaso.

“Ba na rigama da shi, ba ya rigima da ni, muna gaisawa cikin mutunci da kuma ziyartar juna idan akwai sanadi,” in ji shi.

Tsoffin gwamnonin biyu na Kano Malam shekarau da Rabiu Musa Kwankwaso sun taɓa zama inuwa ɗaya a jam’iyyar APC da kuma NNPP ta Kwankwaso kafin Shekarau ya fice jam’iyyar.

Wasu rahotanni kuma na alaƙanta sasanci ne tsakanin ɓangarorin biyu domin buƙatun siyasa.

Sai dai Shekarau ya ce babu wata tattaunawa ta alaƙar siyasa tsakaninsa.

Ya ce suna tattaunawa tun yana APC da kuma bayan ya fice jam’iyyar Kwankwaso ta NNPP.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa