Rundunar ‘yan Sandan Jihar Kano, ta sanya dokar takaita zirga-zirga a kananan hukumomin Ghari, Tsanyawa, Bagwai da kuma shanono.
Kakakin Rundunar na jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya ce an dauki matakin ne domin gudanar da zaben cike gurbi a ranar asabar mai zuwa.
A cewar Kiyawa, ”Dokar za ta fara aiki ne daga 12 na daren Ranar jumu’a zuwa karfe 6 na yammacin gobe Asabar 17 ga watan Augusta, 2025, kuma an haramtawa kowa yawo da makami ko wata alamar jam’iyya a ranar zaben”.
Haka kuma ya ce Rundunar ta shirya tsaf domin samar da ingantaccen tsaro a wadancan kananan hukumomin da za a gudanar da zaben, ta hanyar hada Kai da sauran hukumomin tsaron dake jihar don tabbatar da an yi zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.
A ƙarshe Kiyawa ya ce Rundunar ta kuma haramtawa ‘yan KAROTA da ‘yan vigilante shiga cikin aikin samar da tsaron a kananan hukumomin da za a gudanar da zaben cike gurbin.