Daga Hadiza Nasir Ahmad
Ina hanyar komawa gida ranar Larabar da ta wuce, Ina cikin adaidaita sahu, sai muka biyo hanyar da naga taron wasu gungun mutane, dauke da makaman da ban taba ganin irinsu ba, cike da ruɗani na tambayi direban adaidaita sahun; Me ke faruwa? sai ya ce, “Fadan Daba,” sannan ya kara da cewa, “ki riƙe jakarki sosai.” Ya kara gudu da gaggawa yana ƙoƙarin tserewa daga hatsarin da ke tafe na wadancan yan Daban da suka cike hanya suna sare-sare da kwace.
A nan ne fa direban ya cigaba da mun bayanin yadda yanayin Garin ya koma, ta yadda wadannan Yan Daba ke fita da Rana tsaka suna kwace wayoyi, kuɗi, ko kuma su kashe wanda yaki ba su abinda suke nema. A lokacin ne na fahimci cewa Allah ne ya cece ni ta hanyar dabara da ƙwarewar direban me adaidaita sahun da tuni nima sun mun kwace ko sun illatani.
Raina yayi mutukar baci yadda naga Matasa dauke da wadannan mugayen makamai, yadda mata da yara ke gudu cikin tsoro da kuka.
Na koma gida da mamaki da firgici, na bude wayata, na shiga kafafen sada zumunta, sai naga abun da yake trending kawai shine labarin kwacen waya da daba a kano. Yan Daba sun mamaye Kano, amma gwamnati ta gaza daukar mataki.
Tambayoyi suka ta yawo a raina. Wasu sun ce ‘yan sanda sun daina jin maganar Gwamnatin Jihar Kano, suna sauraron Gwamnatin Tarayya kawai. Wasu kuwa sun ce sai kotu ta ba da umarni tukunna su yi aiki.
Ni dai ina ganin Gwamnatin Tarayya tana ƙoƙari wajen samar da tsaro.
Amma magance matsalar Daba abu ne da yake hannun Gwamnatin jiha.
Wannan ba batun Shari’a bane dake gaban kotu a’a batun rayuka ne. Gwamnatin jihar Kano ba ta da uzuri, dole ne ta daina wasan siyasa da harkar Daba, ta tashi tsaye.
Lamarin kullum sai tsananta yake yi. A na rasa rayuka, amma babu wata magana daga gwamnati, babu kwantar da hankali, babu daukar wani mataki.
Ina ganin ‘yan sanda suna iyakar ƙoƙarinsu. Amma idan gwamnatin jihar ta ci gaba da nuna halin ko-in-kula, ta yi shiru, sannan magoya bayanta suna sukar ‘yan sanda, hakan zai sa ‘yan sandan su gaji, su rasa ƙwarin Gwiwa.
Ya kamata a samu haɗin kai da fahimta tsakanin Gwamnatin jihar Kano da rundunar ‘yan sanda. Gwamna shi ne babban jami’in tsaro na jiha, shi ya fi kowa daukar alhakin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
A baya, mutane sun zargi gwamna Ganduje da ƙyale harkar Daba, duk da cewa ya yi iyaka ƙoƙari sosai wajen dakile su. Amma duk da hakan, ba a yaba masa ba.
Yanzu, matsalar ta ninka sau Uku.
Akwai dalilin da yasa Kano ba ta fada hannun ‘yan bindiga ba, duk da cewa jihohin makwabta suna fama da hakan, ya kamata mu yaba wa Ganduje bisa daukar wasu matakan tsaro da yayi zamanin mulkinsa wanda ake ganin amfanin hakan yanzu.
Akwai lokacin da na je Karamar Hukumar Doguwa, muka wuce ta Dajin Falgore, hanya tayi kyau sosai, an share dajin nayi tambaya, aka ce Ganduje ne ya saka CCTV, har daga ofishinsa yana iya ganin wanda ke shigowa Kano.
Na tuna lokacin da B0k0 Har@m suke yin hare herensu amma saboda haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da na jiha, an fatattake su. B0k0 Har@m basu yi tasiri a Kano ba.
Idan gwamnatin jiha ta ci gaba da wasa da harkar Daba tana siyasatar dashi, za’a haifi wata sabuwar gungun masu laifi ko wata kungiyar tada zaune tsaye da za a kasa shawo kansu.
Akwai wani lokaci da gwamnati ta gana da wasu tubabun yan daba har da yi musu alkawari na canja rayuwa amma shiru kakeji, ta kasa yi musu komai, wannan abin takaici ne matuka.
Gwamnatin jihar Kano ce ke da alhakin hakan kawo matsalar rigimar Daba kuma wajibi ne a gareta ta dauki mataki kafin lokaci ya kure.
Hadiza Nasir Ahmad, Esq
Lauya daga Kano