34.8 C
Kano
Monday, September 8, 2025

Rashin neman izinin gwamna kafin karbar belin Danwawu, shine laifina, wannan ta sa na yi murabus – Kwamishina Namadi

Wannan mataki na murabus ana kallonsa a matsayin ci gaba mai ma’ana da ke nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen tabbatar da gaskiya, adalc, da amintacciyar shugabanci ga al’umma.

A cikin wata sanarwa da Sunusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun Gwamna, ya sanya wa hannu, Kwamishinan ya bayyana cewa ya yanke shawarar ajiye aikinsa ne saboda muhimmancin al’amuran da ke tattare da batun da ake magana akai

Alhaji Namadi ya nuna godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya ba shi na yin aiki, yana mai jaddada aniyarsa ta ci gaba da bin akidar kyakkyawar shugabanci da natsuwa a jagoranci.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi murabus ɗin cikin girmamawa tare da yi masa fatan alheri a rayuwarsa ta gaba.

Gwamnan ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da yaƙi da laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi da sauran ɗabi’un banza da ke addabar matasa da al’umma gaba ɗaya.

Ya kuma ja kunnen sauran masu mukaman siyasa da su riƙa taka-tsantsan a duk wani lamari da ya shafi al’umma, tare da nema izini daga manyan hukumomi kafin su ɗauki mataki a irin waɗannan al’amura.

A wani takaitaccen hoton bidiyo da tsohon kwamishinan ya fitar yace laifin da daya da kwamatin binciken sa ya gano shine rashin tuntubar gwamna Yusuf kafin yanke hukuncin belin Danwawu din.

Yace abin ya zame masa darasi a yanzu cikin rayuwarsa.

Ya sake neman afuwar jama’ar Kano da masoyansa musamman damuwa da su ka shiga.

Namadi Dala ya kuma godewa Allah abisa yadda kwamatin bai kamashi da wani laifi ba musamman zarge zargen karbar cin hanci da rashawa kan maganar belin,illa dai rashin neman izinin gwamna Yusuf kafin karbar belin Danwawu

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa