14.9 C
Kano
Sunday, January 18, 2026

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Harkokin Cikin Gida Da Hadin Guiwar Cibiyar horas Da Yan Jarida Sun Fara Horas Da SSR Da SR Na Kwana 4

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Harkokin Cikin Gida Da Hadin Guiwar Cibiyar horas Da Yan Jarida ta kasa sun fara Horas da jami’an watsa labaran gwamnatin Kano SSR Da SR Na Kwana 4, a jami’ar Bayero dake Kano a dakin taro na Aliko Dangote yau Litinin.

Da yake tattaunawa da yan jarida Kwamishinan yaɗa labaran jihar Kano da harkokin cikin gida ya bayyana cewar wannan babbar nasara ce ga jihar Kano da gwamnatin jihar

Ya kuma bayyana cewa, taro ne na horas da jami’an gwamnati wadanda suke dauko rahotanni na mai girma Gwamna, waɗanda ake kira da SSR Da SR domin su kara samun horo irin na yan jarida, domin yanzu aikinsu yana kama da na yan jarida, domin su tantacewa da yaɗa sahihan labarai, shi yasa mai girma Gwamna ya bada umarnin a basu wannan horon na musamman domin kara samun kwarewa wajen aikinsu wadanda suka kai yawan 135

Camarde Waiya ya bayyana cewar wannan horaswa ce da aka yi haɗin gwiwa da International Institute Of Journalist da kuma AUSAM Communication LTD wanda za a kwana 4 ana gabatarwa, kuma idan an kammala za a basu shaidar wannan horo.

Kwamishina ya kuma bayyana cewar bayan gabatar da wannan horo ana sa ran samun sauyi a garesu kamar yadda aka samu a kan jami’an yaɗa labarai na kananan hukumomi wajen iya yaɗa labarai yadda ya kamata bayan zuwanmu.

Ya kuma karawa da cewa, muƙamin SR da SSR mai girma Gwamnan Kano Abba Kabir ne ya fara samar da shi, domin samar da gurbin aikin yi ga matasa duba da galibinsu matasan ne, sannan kuma wannan horan zai taimaka musu wajen maganace labaran kanzan kurege, za suyi aikinsu kamar Yan jarida.

Shima a nasa bangaren wakilin gwamnan Kano kuma shugaban ma’aikatan jihar Kano Abdullahi Musa ya bayyana jin dadinsa ganin yadda matasan suka Mai da hankali wajen wannan horan.

Ya kuma bayyana musu cewar ya kamata su san dalilin da yasa aka basu wannan muƙamin, zai taimaka musu wajen gudanar da ayyukan masu.

Musa yayi kira ga ɗaukacin SSR da SR da sauran maaikatan jihar Kano su zamo masu rikon amana da maida hankali akan ayyukan su domin haduwa da Allah lafiya

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa