Daga Abba Anwar
Da farko ya zama dole a yabawa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu saboda mayar da Babbar Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Gwamnatin Tarayya ta Kabo zuwa ga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kabo. Abinda kamar yadda a ka ce, ba a taba samun wani shugaba ya yi haka cikin kankanin lokaci ba.
Bayan hobbasa da kokarin gaske da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta Kasa, Sanata Barau Jibrin CON, ya yi wajen samar da wannan Babbar Makarantar, a shiyyar Kano ta Arewa, canza sunan Babbar makarantar da ba ta matsayin Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Gwamnatin Tarayya, wata manuniya ce ta kyakkyawar alakar da ke tsakanin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da kuma Sanata Barau.
Tun yanzu tun ba a je ko ina ba, shugaban kasa Tinubu ya na nuni da cewar alakarsa da Sanata Barau mai kyau ce kuma zartacciya. Wacce yanayi ya nuna za su iya aiki tare dan ci gaban kasar nan. A dukkan matsayin da mai karatu zai iya tunani.
Kamar dai yadda Sanatan da kansa ya nuna, a cikin shekaru biyu kacal Shugaba Tinubu ya samar da manyan makarantu guda biyu ga jihar Kano. Bayan daga likkafar babbar Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya ta Kano, zuwa ga matsayin Jami’a. Wacce a da an taba mayar da ita Jami’a amma wasu dalilai na siyasa su ka sa a ka soke hakan. Amman Tinubu ya dawo da waccan daga martabar da a ka soke. Duk bisa kokarin Sanata Barau da abokan aikin sa ‘yan majalisa.
Tare da kuma canza mata suna zuwa ga Jami’ar Ilimi ta Yusuf Maitama Sule. Dan tunawa da mazan jiya tare da rike sunan sa a cikin al’umma saboda irin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban Arewa da kuma kasa gaba daya.
Sai kuma ita Jami’ar Fasaha da Kimiyya ta Kabo ga kuma Kwalejin Tarayya ta Kimiyya da Fasaha ta Rano. “Wannan ba karamin kyakkyawan baya shugaban kasa ya kafa ba a wannan jihar ta mu ta Kano, ” in ji Sanata Barau.
Kalli dai irin babban kokarin da Sanata Barau ya yi fa tun daga matakin Majalisa zuwa ga sahalewar da shugaban kasa ya bayar na mayar da Babbar Makarantar Fasaha da Kimiyya ta Kabo zuwa Jami’ar Fasaha da Kimiyya.
Shi da kan sa Sanatan ya ce “A cikin wata biyu da su ka wuce na gabatar da kudurin neman a mayar da Babbar Makarantar Tarayya ta Fasaha da Kimiyya ta Kabo zuwa Jami’ar Tarayya ta Fasaha da Kimiyya ta Kabo. Wanda ina godewa majalisun mu na Dattawa da na Wakilai. Wanda a cikin wata biyu kacal su ka yarda da wannan kundin kudurin.
Abinda ya rage mana shine samun sahalewar shugaban kasa kan ya sa hannu a mayar da abin ya zama doka. Kafin ma majalisa ta kai masa wannan kudurin na samu shugaban kasa na yi masa bayanin muhimmancin mayar da makarantar ta zama Jami’a.
Bayan ya yi alkawarin zai sa hannu bisa hakan. Da kai masa kuduri ba tare da bata wani lokaci ba, ya rattaba hannu a kai. Kamar yadda ya yi alkawari.”
Sanatan ya ci gaba da cewa,” Na nunawa shugaban kasa muhimmancin samar da ilimin kimiyya da fasaha ga matasan mu. Wanda Kano ce ta fi kowace jiha yawan matasa a kasar nan. Saboda haka ya zama wajibi da kodayaushe a tallafawa neman ilimin su.
Ba fa wannan ne kawai abubuwan dubawa ba a wannan babban kokari da Sanata Barau ya yi na mayar da wannan makaranta zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ba, akwai maganar an samar da wani yalwataccen bigire na samarwa da jama’a aikin yi. A halin da a ke ciki na rashin ayyukan yi ga matasa.
Sannan kuma irin kwasa-kwasan da za a karanta a wannan makaranta na bagarorin kimiyya da fasaha, wanda abinda zamani ke nema kenan ruwa a jallo, su ma su na nuni ga yadda al’umma za su amfana matuka da gaske.
Hatta kayan aiki da samar da yanayi mai kyau ga wannan jami’a dan cimma babban burin kafa ta, Sanatan ya yi alkawarin ci gaba da jajircewa wajen ganin ta mike sosai ta amsa sunan ta na jami’a.
Ya ce zai ci gaba da bibiyar ganin an samar da malamai da kuma yanayi mai kyau na koyo da koyarwa. Hatta ci gaba da gine-gine dan samun gamsassun wurare da kuma bangarori na yin karatu cikin kwanciyar hankali da nutsuwa a cikin zuciyar malamai da dalibai da kuma ma’aikatan wannan jami’a.
Irin hangen nesan da Sanata Barau ke nunawa wajen tafiyar da wannan ofis na sa na dan majalisar dattawa mai wakiltar Kano ta Arewa, da kuma babban mukamin da yake rike da shi na Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, kullum ya na kara haska mana waye Sanatan. Wakili na gari, wanda yake amfani da ilimi wajen tafiyar da harkokin sa na wakilci. Ga kuma dattako da sanin ya kamata.
Bayan yabawa da Sanatan ya yi ga shugaban kasa wajen wannan abin alheri na mayar da makarantar zuwa jami’a, ya ci gaba da cewa, “Kamar yadda kowa ya sani ne cewar su fa matasa sune kashin bayan ci gaban kowace irin al’umma.
Saboda haka kokarin da mu ka yi na mayar da wannan makaranta zuwa jami’a abu ne da ya dace da bukatun zamani na harkokin ci gaban al’umma. Ya zama dole mu yi duk mai yiwuwa wajen ganin mun ba matasan mu goyon baya da dukkan tallafin da ya kamata na su bayar da ta su gudummawar na ci gaban kasa. Dan mu gudu tare mu tsira tare.”
Ga dukkan mai lura da al’amuran yau da kullum zai fahimci cewar Sanata Barau ya na da tsahon da zai iya yi wa jama’arsa aiki a ko ina ne cikin fadin kasar nan.
Idan ka kalli abubuwan kawo ci gaba da yake ta kwararowa al’ummar sa ba kakkautawa ka san lallai wannan shugaba ne mai sanin ya kamata. Kuma Jagora ne mai iya fahimtar bukatun al’ummar da su ka tura shi wakilci a Abuja. Ba wai ba inke!
Anwar tsohon Babban Sakataren Yada Labarai ne na tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje CON, za kuma a iya samun sa a fatimanbaba1@gmail.com
28 ga Watan Mayu, 2025


