Gwamnatin Tarayya Zata Hana Manyan Motoci Dakon Kaya Da Daddare a fadin kasar
Ra’ayoyi mabanbanta na cigaba da cin karo da juna biyo bayan sanarwar da gwamnati ta yi na cewa ba za a sake barin tankokin dakon mai su cigaba da yin aiki da daddare ba.
Wannan shawara na da nasaba da kokarin da gwamnatin kasar ke yi na rage munanan hadurran fashe-fashe da tankokin mai dauke da man fetur wanda ke haddasa asarar rayuwa da dukiyoyi.
Shin wannan haramcin zai iya kawo karshen matsalolin tashin gobarar tankokin mai a hanyoyi?


