27 C
Kano
Sunday, January 18, 2026

Gwamnatin Tarayya Ta Soke Faretin Ranar Dimokuraɗiyya

Gwamnatin tarayya ta soke faretin sojoji da ake gudanarwa a duk shekara domin bikin Ranar Dimokuraɗiyya, wanda aka saba yi a ranar 12 ga Yuni.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamitin haɗin gwiwa na ma’aikatun gwamnati da ke kula da shirye-shiryen bikin ya fitar, inda ya tabbatar da cewa ba za a gudanar da faretin a bana ba, sabanin yadda aka saba a shekarun baya.

A cewar kwamitin, maimakon faretin, za a gudanar da wasu shirye-shirye na musamman da suka haɗa da jawabin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da misalin ƙarfe 7:00 na safe. A cikin jawabin, ana sa ran shugaban zai yi nazari kan yadda dimokuraɗiyya ke tafiya a ƙasar, da irin ƙalubalen da ake fuskanta, da kuma matakan da gwamnati ke ɗauka wajen ƙarfafa tushen dimokuraɗiyya da kyautata shugabanci.

Daga bisani, da ƙarfe 12:00 na rana, shugaban ƙasa zai halarci wani zama na musamman tare da majalisar dokoki ta ƙasa, domin tattaunawa kan muhimman batutuwa da suka shafi ci gaban demokuraɗiyya da haɗin kan ƙasa.

Haka kuma, da ƙarfe 4:00 na yamma, za a gudanar da babban taron ilimi a Dandalin Taro na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ƙarƙashin taken: “Ƙarfafa Dimokuraɗiyya Ta Hanyar Gyare-gyare Masu Dorewa.” Taron zai haɗa manyan jiga-jigan siyasa, masana, da wakilan ƙungiyoyin farar hula, domin nazari da tattaunawa kan ci gaban dimokuraɗiyya a Najeriya.

Sai dai ko da yake ba a fitar da cikakken bayani kan dalilin soke faretin ba, wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta ce akwai yiwuwar hakan ya samo asali ne daga abin da ya faru a shekarar da ta gabata, inda shugaban ƙasa Tinubu ya yi tuntuɓe yayin da yake ƙoƙarin hawa motar faretin a filin Eagle Square

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa