Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 31 ga Maris, da Talata, 1 ga Afrilu, a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Sallah Ƙarama
Ministan Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Magdalene Ajani, Babbar Sakatariyar Ma’aikatar, ta fitar a ranar Laraba.
Ministan ya taya daukacin al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, tare da yin kira ga al’ummar 3su rungumi dabi’un hakuri, tausayi, kyauta, da zaman lafiya.
Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya su yi amfani da wannan dama wajen yin addu’o’i don zaman lafiya, daidaito, da ci gaban kasa.
Tunji-Ojo ya yi fatan cewa wannan biki na Sallah Ƙarama zai kara hadin kai da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai da kabilu daban-daban a kasar.
A karshe, ya bukaci jama’a da su yi bukukuwa cikin lumana da kiyaye doka, tare da tunawa da marasa galihu ta hanyar ayyukan alheri .
Gwamnati ta kuma aika da fatan alheri na Eid Mubarak ga daukacin al’ummar Musulmi, tana mai addu’ar Allah Ya kawo albarka, nasara.


