Gwmanan jihar Edo a Najeriya, Monday Okpebholo, ya dakatar da Kwamandan Rundunar Samar da Tsaro a jihar Friday Ibadin, biyo bayan kisan da aka yi wa mafarauta 16 ƴan asalin yankin arewacin kasar a alhamis da ta gabata.
A wata Sanarwar gwamnati ta ce an ɗauki matakin ne ta la’akari da bayanan da ke ƙunshe a rahoton binciken farko da aka gudanar dangane da wannan lamari, wanda ya yi matuƙar girgiza jama’a a Najeriya.
‘’ Lura da abubuwan da suka faru a ranar ta 27 ga watan Maris na 2025 a garin Uromi na ƙaramar hukumar Esan, inda aka samu asarar rayukan wasu matafiya, Mai Girma gwamna Monday Okpebholo, ya bayar da umurnin dakatar CP mai ritaye Friday Ibadin, Kwamandan Rundunar Samar da Tsaro ta jihar daga matsayinsa.’’ a cewar sanawar.
Har ila yau, sanarwar wadda kafafen yaɗa labarai a Najeriya suka wallafa ɗauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin jihar ta Edo Musa Ikhilor, ta ƙara da cewa an rusa illahirin ƙungiyoyin ƴanbanga da ba su da rajista a jihar, biyo bayan wannan kisa.
Sanarwar ta ci gaba da cewa ƴanbangar da suka aikata wannan ta’asa, suna aiki ne ƙarƙashin inuwar wata ƙungiya da ba ta da rajista, saboda haka ya zaman wajibi a ɗauki wannan mataki don tabbatar da samar da yanayi na tsaro a jihar