Fitacciyar Jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood Hajiya Saratu Gidado Wadda aka fi sani da Daso ta Rasu tana da shekaru 56 a duniya.
Rahotanni sun ce marigayiyar ta Rasu kumanin sa’o’i biyu da Suka gabata kamar yadda majiyoyin kusa da iyalanta Suka tabbatar.
Majiyoyin sun ce za a yo jana’izarta da karfe 4 na yammacin yau.
Har yanzu dai Babu cikakken bayani game da musabbabin rasuwar ta.