Rahotanni daga Nigerian Tracker sun tabbatar da cewa za a gudanar da sallar jana’izarsa a gidansa da ke Janbulo, cikin birnin Kano.
Marigayi Getso ya shafe shekaru da dama yana aikin jarida, inda ya yi aiki da manyan gidajen rediyo da dama a Kano, ciki har da Radio Kano, Freedom Radio, Vision FM, da Premier Radio, inda ya taka muhimmiyar rawa a fannin editing da fassarar labarai.
Aliyu Getso ya kasance ɗaya daga cikin fitattun masu ba da gudummawa wajen bunƙasa aikin jarida a Kano da ma Arewa gaba ɗaya. Abokan aikinsa da dama sun bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga masana’antar yada labarai a Najeriya.
Allah Ya jikansa da rahama, Ya ba iyalansa da abokan aikinsa haƙuri da juriya.


