31.1 C
Kano
Monday, September 8, 2025

Farfesa Hafsat Ganduje ta gwangwaje dubban kanawa da tallafin azumi

Kamar yadda ta saba yi kowacce shekara a bana ma Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ta rarraba shinkafa tare da kudaden ga yayan jamiyyar Apc dake kananan hukumomi 44 dake Kano

Da take kaddamar da fara rabon a yau shugabar matar jamiyyar APC ta Kano Hajiya Fatima Abdullahi Dala ta bayyana cewa rabon ya shafi shugabannin matan jamiyyar ta APC da mawallafa na jamiyyar hadi da yan social media da matan jamiyyar da sauran al’umma.

Hajiya Fatima Dala ta ce Farfesa Hafsat Ganduje ta damu matuka da son farantawa alummar Kano adon haka tace zata cigaba da tallafa musu da sanya su cikin walwala.

Taron dai ya samu halartar masu ruwa da tsaki na jamiyyar ta APC da dama daga kananan hukumomi 44 na Kano.

Farfesa Hafsat Ganduje dai wacce uwargidan tsohon gwamnan Kano ce kuma a yanzu haka uwargidan shugaban jamiyyar APC na kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje ta yi fice a zamanin da suke Mulkin gwamnatin Kano wajen zagayen kananan hukumomi 44 don tallafawa mata da matasa da kudade da kayayyakin sanaoi’n dogaro da kai.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa