31.1 C
Kano
Sunday, January 18, 2026

Fadan Daba a Kano siyasa ce ,daga yan adawa domin batawa gwamnati suna – Gwamnatin Kano

Saidai gwamnatin Kano ta alakanta fadan dabar da siyasa,da take zargin wasu yan hamayya da rura rikicin dabar domin bata sunan gwamnati.

Kwamishinan kananan hukumomi na Kano,Hon Muhammad Tajuddeen othman shine ya bayyana hakan a lokacin da ake tambayarsa kokarin da gwamnatin kano keyi na magance fadan Daba ta cikin shirin”Gwamnati da jama’a”da aka gudanar a tashar Rahma Radio da ke Kano.

Kwamishinan ya yi zargin wasu daga cikin yan siyasa da daukar nauyin fadan Dabar a birnin Kano domin cimma wata manufa tasu ta siyasa.

Hon. Tajuddeen othman ya tabbatarwa da jama’ar Kano cewa gwamnati na iya kokarin ta wajen magance matsalar ta hanyar daukar matasa aikinyi da sanyasu a makarantu.

TST Hausa ta rawaito cewa, kwamishinan ya kuma shaida cewa kwamatin da gwamnatin kano ta kafa na magance fadan Daba karkashin jagorancin kwamishinan ma’aikatar kimiya da fasaha Dr Yusuf Ibrahim Kofar Mata na aiki dare da rana domin samar da tsaro a Kano.

Idan za’a iya tunawa daga ranar laraba zuwa safiyar Juma’a da Asabar fadacen fadacen dabar da kwacen waya yayi salwantar rayuwakan matasa biyu a birnin Kano ,Inda kuma fadan dabar ya hana jama’a sakat a cikin birnin.

Kwamishinan ya shaida cewa tabbatar da kare rayukan jama’a da dukiyoyin mutanan Kano na daga cikin kudurin gwamna Abba Kabir Yusuf tun kafin hawansa mulkin Kano

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa