29.1 C
Kano
Monday, September 8, 2025

Duk Jami’in Gwamnatin Da Ba Zai Iya Sauke Nauyin Da Ke Wuyansa Ba Ya Ajiye Aikinsa – Gwamnan Kano

Biyo bayan murabus da Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Namadi Dala, ya yi sakamakon shigar sa cikin batun beli na wani da ake zargi da laifin miyagun ƙwayoyi, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi gargaɗi mai ƙarfi ga dukkan jami’an gwamnati da ke ƙarƙashin mulkinsa.

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa na da ƙuduri na yakar shaye-shaye, fataucin miyagun ƙwayoyi, da duk wani ɗabi’ar da ke barazana ga rayuwar matasa da makomar jihar.

A wajen taron Majalisar Zartarwa karo na 30 da aka gudanar a Fadar Gwamnati ta Kano, Gwamna Yusuf ya bayyana rashin jin daɗinsa kan al’amarin, inda ya shawarci mambobin majalisa da su kasance masu gaskiya da amana a aikinsu.

Ya bayyana cewa murabus ɗin Kwamishinan ya zama izina ga duk wani jami’in gwamnati, yana mai cewa:

“Ba za mu yarda da kowanne irin hali da zai yi wa gwamnatin nan tarnaki ba, ko a aiki ne ko a rayuwar sirri.”

Gwamnan ya ƙara da cewa duk wanda bai da ikon ɗaukar nauyin amana da aka dora masa, zai fi dacewa ya yi murabus cikin kima, maimakon ya shiga halin da zai ɓata suna da mutuncin gwamnati.

Ya kuma sake jaddada cewa yaƙi da miyagun ƙwayoyi da sauran mummunan ɗabi’u wani muhimmin ginshiƙi ne a mulkinsa, kuma duk wanda aka samu yana taimaka wa irin waɗannan laifuka zai fuskanci hukunci mai tsanani.

A ƙarshe, ya jaddada aniyar gwamnatinsa wajen tabbatar da adalci, gaskiya, da tsantsar hidima ga al’ummar Kano.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa