Tsohon Shugaban karamar hukumar Bichi Dr Yusuf Muhammad Sabo ya taya dan majalisar tarayya mai wakilyar yankin karamar hukumar Bichi Injiniya Abubakar Bichi murna bisa zagayowar ranar haihuwarsa
Dr Sabo ya bayyana injiniya Abubakar Kabir Bichi a matsayin shugaba nagari kuma abin koyi ga yan siyasa dake tasowa
Yace jajircewarsa wajen kawo cigaba da aka dade ba’a samu ba a yankin Kano ta Arewa musamman karamar hukumar Bichi da kuma jihar Kano gaba daya abin alfahari ne
Yayi Adduar samun Karin shekaru masu albarka ga dan majilasar da tarin nasarori


