24.7 C
Kano
Monday, January 19, 2026

Da Dumi Dumi; Major Hamza Al Mustapha ya koma jamiyyar SDP

Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a hukumance, matakin da ke nuna sabon shiri na inganta ci gaban kasa.

Tare da rakiyar tawagarsa, Al-Mustapha ya isa hedkwatar jam’iyyar SDP da ke Abuja, inda shugabanni da magoya bayan jam’iyyar su ka tarbe shi da farin ciki. Shigarsa jam’iyyar na nuni da kudurinsa na jagoranci bisa adalci, tsaro, da ci gaba.

Shugabannin SDP sun bayyana fatansu cewa Al-Mustapha zai karfafa manufofin jam’iyyar na hada kan kasa da samar da ingantaccen shugabanci.

Yayin da jam’iyyar ke ci gaba da fadada tasirinta, shugabanninta sun jaddada kudurinsu na gina tafiyar siyasa mai karfi da za ta canza alkiblar kasar nan.

Hamza Almustapha shi ne babban jami’in tsaron da ke kula da fadar shugaban kasa a zamanin Janar Sani Abacha.

Hamza Almustapha dai na daga cikin makusantan marigayi Janar Sani Abacha musamman a lokacin da ya yi shugaban Nijeriya na mulkin soja daga shekarar 1993-1998.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa