Jigo a Jamiyyar APCn jihar Kano Honourable Muntari Ishaq Yakasai ya ce jamiyyar APC zata karbi ragamar mulkin Kano a kakar zaben shekarar 2027 cikin sauki ba tare da wata wahala ba
Muntari Ishaq Yakasai ya bayyana hakan a zantawarsa da Jaridar Daily Watch 24
Yace jamiyyar Adawa ta NNPP ta na kan hanyar rugujewa duba da yadda a kullum suke fama da rikicin cikin gida Wanda ke haifar musu da koma baya
Yace jamiyyar APC kullum gaba takeci duba da yadda jamaa ke tururuwar komawa cikin jamiyyar
Muntari Ishaq Yakasai ya kuma ce ko yanzu anga bambancin mulkin APC dana NNPP kasancewar gwamnatin Kwankwsiyya Tana mayar da Kano baya.