Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ce shirin kafa jam’iyyar haɗaka da ake son yi, ba barazana ba ce ga shugaba Bola Tinubu.
Ya ce hakan bai nuna cewa akwai wata barazana da za ta tinkari jam’iyyar APC ba.
“Zan faɗa muku, sannan ku je ku rubuta. Babu wata barazana da Tinubu ke fuskanta,” kamar yadda gwamnan ya bayya a shirin siyasa na Politicis Today na gidan talabijin na Channnels ranar Juma’a.
Gwamnan yana mayar da martani ne kan kafa wata ƙungiya mai suna National Opposition Coalition Group, wanda tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark ke jagoranta.
Ya ƙara da cewa yawancin waɗanda ke goyon bayan haɗakar ba su san irin ƙoƙari da masu fafutuka suka yi ba wajen ganin tabbatuwar dimokraɗiyya da kuma shugabanci na gari a Najeriya.
“Mutanen da ke magana a yau, ina suke lokacin da ake fafutikar samun dimokraɗiyya, adalci, shugabanci na gari da kuma doka? Ba su san komai game da hakan ba.
Gwamnan ya kuma ce ba ya fargabar ƴan adawa a jihar ta Kaduna saboda irin yadda gwamnatinsa ke yin ƙoƙari.


