23.1 C
Kano
Friday, January 16, 2026

Babu abin da gwamnatin Tinubu ta sani sai ƙarin kuɗin fetur – NLC

Kungiyar kwadago a Najeriya NLC ta bayyana kaduwa kan karn farashin litar man fetur da aka wayi garin Laraba da shi a kasar.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Kwamared Joe Ajero, ya ce alamu sun nuna babu abin da wannan gwamnatin ta sani “face kara kudin man fetur ba tare da tuntubar kowa ba, ba kuma tare da an wadata ‘yan kasar da hanyoyn rage radadi ba”.

BBC ta ruwaito Sanarwar ta ci gaba da cewa tsame hannun da kamfanin mai na kasa NNPCL ya yi tsakanin ‘yan kasuwa da matatar mai ta Dangote abin dubawa ne.

“Ya kamata gwamnati ta sake nazari ta kuma gabatar mana shirin da take yi na bunkasa tattalin arzikin Najeriya, da ci gaban kasa maimakon daukar matakan da ba su wani tasri sai dagula lamurra,” in ji NLC.

A ranar Laraba ne aka wayi gari kamfani NNPCL ya kara farashin man a karo a biyu cikin wata guda.

A birnin tarayya Abuja, sabon farashin lita daya ya fara daga naira 1,030, sabanin yadda ake sayar da shi a baya kan naira 897

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa