Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada umarninsa ga jami’an tsaron ƙasar nan da su yi duk mai yiwuwa don kuɓutar da ɗaliban makarantar Kuriga da ‘yan bindiga suka sace a makon da ya gabata.
BBC ta ruwaito cikin wani jawabi da ministan yaɗa labaran ƙasar nan Mohammed Idris ya yi wa manema labarai, jim kaɗan bayan taron majalisar zartarwar ƙasar da aka gudanar a fadar gwamnati, ministan ya ce gwamnati ba za ta biya ko sisin kobo ba a matsayin fansa ga maharan don sakin ɗaliban.
Ministan ya ce gwamnatin ƙasar ba za ta lamunci ci gaba da sace ɗalibai don yin garkuwa da su ba, don haka ya ce gwamnati ke kira ga jami’an tsaron da su yi duk abin da ya kamata don tabbatar da sakin ɗaliban da sauran mutanen da hannun ‘yan bindiga a faɗin ƙasar.
”Idan ta kama gwamnati za ta yi amfani da ƙarfin tuwo wajen kuɓutar da ɗaliban nan, saboda hukumomin tsaronmu a shirye suke ko me za a yi a dawo da waɗanna ɗaliban”, in ji shi.