Wata sanarwa ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin Farfesa Sambo Wali Junaidu ta ce Sarki Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin musulunci a Najeriya ya amince da rahoton kwamitin Kuma ya nemi Musulmin Najeriya su cigaba da azumi ranar Lahadi.
Saboda haka ya yi matsaya cewa watan Ramadan zai cika kwanaki 30 kuma ranar litinin 31 ga watan Maris ita za ta kasance 1 ga watan shawwal kuma ranar sallah karama a Najeriya
Ba wannan ne karon farko da ake yin Azumi talatin ba a Najeriya inda ko a shakerar data gabata azumi 30 akayi.